Cibiyar Zhongshan da aka kafa a ranar 26 ga watan Fabrerun 1989, ita ce cibiyar binciken kimiyya ta 2 cikin 4 da kasar Sin ta gina a yanki mafi kankara na biyu a duniya dake nahiyar Antartica, tun 1964. Kuma a yanzu, ita ce cibiyar dake samar da hidimomi ga ayyukan bincike a nahiyar mai kankara.
A cewar ayarin masu binciken, cikin sama da shekaru 30, Zhongshan ta habaka zuwa cibiyar kimmiya ta zamani a nahiyar, wadda kan iya samar da hidimomi ga jiragen sama masu nauyi. (Fa'iza Mustapha)