in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin zai kai ziyara Turai
2019-04-02 19:47:16 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya shaidawa taron manema labarai a yau Talata cewa, firaministan kasar Li Keqiang zai kai ziyara Turai daga ranar 8 zuwa 12 ga watan Afrilu, inda ake saran kuma zai halarci taron shugabannin Sin da kungiyar tarayyar turai karo na 21 da zai gudana a birnin Brussels, da taron shugabannin Sin da kasashen gabashi da tsakiyar Turai karo na 8 da zai gudana a Croatia, da kuma ziyarar aiki da zai kai kasar.

Bugu da kari, Li zai ziyarci kasashen na Turai ne bisa yarjejeniyar da bangaren Sin da Turai suka cimma, kana bisa gayyatar da firaministan Croatia Andrej Plenkovic ya yi masa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China