in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya tattauna da wakilan kungiyar BOAO
2019-03-30 15:59:26 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tattauna da wakilai daga bangarorin kasuwanci da harkokin kudi da yada labarai da kwararrun dake halartar taron shekara, na kungiyar BOAO na nahiyar Asiya.

Li Keqiang, ya bayyana yayin taron da ya samu mahalartar sama da 200 daga fadin duniya cewa, rungumar manufar aiwatar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, zabi ne da al'ummar kasar Sin suka dauka bisa radin kansu.

Ya ce cikin sama da shekaru 40 na aiwatar da manufar, al'ummar kasar sun samu kwararan alfanu, sannan kasar za ta kara fadada bude kofarta.

Ya ce gwamnatin kasar Sin na tabbatar da daidaito tsakanin kamfanonin cikin gida da na baki, kana tana kare hakkin mallakar fasaha kamar yadda doka ta tanada.

Bugu da kari, Firaministan na kasar Sin, ya ce nan ba da dadewa ba, kasar za ta dauki matakan rage lokacin da ake dauka kan a amince da magunguna da shigarsu kasuwa, domin amfanawa marasa lafiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China