in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya lashi takobin kara inganta karfin kasuwar kasar
2019-03-26 09:28:55 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da wakilan kasashen waje dake halartar taron ci gaban kasar Sin na shekarar 2019, inda ya lashi takobin amfani da manufar bude kofa da gyare-gyare domin ingiza karfafa kasuwa da tabbatar da yanayi mai kyau ga habakar tattalin arzikin kasar Sin.

Wakilan sun hada da shugabannin manyan kamfanoni 500 na duniya, da malamai daga fitattun cibiyoyin bincike da wakilai daga hukumomin kasa da kasa.

Li Keqiang ya ce, baki daya, kasar Sin ta samu kwakkwaran ci gaba yayin da kuma ta samu bunkasar tattalin arziki a bara. Ya ce yayin da ake fuskantar sabon matsi, kasar Sin za ta ci gaba da aiki tukuru wajen daukar matakan kandagarki kamar na haraji da samar da sabbin dabarun ci gaba.

Ya ce, manufar majalisar wakilan jama'ar kasar ta amincewa da dokar zuba jari na baki ita ce, kyautata kare jarin waje a kasar Sin bisa doka.

Wakilan sun bayyana tabbaci game da kasuwar kasar Sin, suna cewa za su fadada cinikayya da zuba jari a kasar domin kara samun damarmaki daga ci gabanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China