Yau Alhamis 28 ga wata, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya ce, kamata ya yi sassa daban daban su hada kansu domin samun ci gaba tare, su kiyaye tsarin kasa da kasa, da ba da muhimmanci ga MDD, su kuma tabbatar da tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa ka'idoji. Kasar Sin na kira da a yi ciniki cikin 'yanci da adalci. Kamata ya yi sassa daban daban su kara azama na ganin an yiwa tsarin tafiyar da harkokin duniya gyare-gyare, a kokarin ganin an tafiyar da harkokin duniya cikin adalci. Kana kasar Sin na goyon bayan yin kwaskwarima ga kungiyar ciniki ta duniya wato WTO, amma tilas ne a ci gaba da martaba ka'idoji da muhimman akidun kungiyar.
Har ila yau firaministan kasar Sin ya ce, kasar Sin tana nan tana tsara dokoki masu alaka da dokar zuba jari ta 'yan kasuwa baki don aiwatar da dokar yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)