Afrika ta kasance nahiyar da aka fi fama da kamfar abinci a duniya, yayin da kusan ake samun mutum guda daga cikin mutane 4 dake fama da karancin abinci mai gina jiki, in ji kungiyar ta AU.
A cewar kungiyar ta Afrika, a shekaru masu yawa, mafi yawan kasashen Afrika suna mayar da hankali ne wajen kara samar da abinci, amma a cewar AU, yawan abincin da ake tafka hasara a duk shekara ya zarta hatsin da ake shigowa da shi daga kasashen ketare zuwa Afrikar.
Wannan matsalar hasarar abincin da ake samu tana matukar haddasa karancin abinci kuma tana da mummunan tasiri ga muhalli ta hanyar lalata filaye da ruwa, da kayayyakin aikin gona da makamashin da ake amfani da shi wajen samar da abincin, in ji kungiyar ta AU. (Ahmad Fagam)