in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga kasashen Afrika su kara shiga ana damawa da su a duniya domin gaggauta samun sauyin fasaha zuwa ta zamani
2019-03-30 15:54:24 cri

Tarayyar Afrika AU, ta jaddada bukatar nahiyar ta kara daga muryarta da kasancewa cikin yarjeniyoyin duniya kan batutuwan da suka shafi sarrafa bayanai da tsaron intanet da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.

Tarayyar AU, wadda ta ce fasahar wayar tafi da gidanka ta taimakawa nahiyar tafiya da zamani, musammam cikin shekaru 10 da suka gabata, inda ta jaddada cewa, batun sauyawar fasaha zuwa na zamani, ya kasance muhimmin batu a tarukan da suka gudana tsakanin shugabannin nahiyar, karkashin inuwarta.

Da take kara kira ga nahiyar da ta karfafa zuba jari kan fasahar zamani, Tarayyar ta ce kasashen dake fadin nahiyar na samun ci gaba, ta hanyar amfani da ingantacciyar fasahar zamani a fannonin ilimi da aikin gona da ci gaban tattalin arziki da dai sauran wasu bangarori.

Tarayyar mai mambobi 55 ta yi kiran ne lokacin kaddamar da jerin tattaunawa kan hadin gwiwa a fannin fasahar zamani na nahiyar Afrika wanda kwamitin manyan jami'ai na MDD kan hadin gwiwa a fannin ya yi.

Kwamitin na manyan jami'ai kan fasahar zamani, tawaga ce ta kwararru mai zaman kanta, wadda Sakatare Janar na MDD ya dorawa nauyin fadada tuntuba kan damarmakin da kalubalen dake tattare da hadin gwiwa a wannan zamani na fasaha.

A cewar AU, taron zai mayar da hankali ne kan tattaunawa da lalubo fannonin gaggauta hadin kai tsakanin kasashen Afrika da kamfanoni da bangarori, da kuma hada karfi da karfe wajen samar da ingantattun dabarun ciyar da fannin fasahar zamani gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China