in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta kaddamar da wani tsarin tabbatar da dorewar sarrafa kayayyaki bisa kare muhalli
2019-03-09 16:49:34 cri
Tarayyar Afrika ta kaddamar da wani tsarin tabbatar da inganta dorewar sarrafawa da amfani da kayayyaki bisa kare muhalli.

Shugaban sashen kula da harkokin gona da wadatuwar abinci na hukumar tarayyar, Simplice Nouala, ya shaidawa manema labarai a Nairobin Kenya cewa, tsarin wanda ya samar da tambarin da aka yi wa lakabi da EcoMark, wani matakin inganci ne na kayayyakin nahiyar baki daya, a fannonin yawon bude ido da aikin gona da kiwon kifi da bangaren kula da dazuka.

An tsara tambarin ne domin kayayyaki da hidimomin da suka cimma ka'idojin da aka tanada kan muhalli da al'umma da tattalin arziki da dokoki.

Ya ce tabbatar da EcoMark zai bada gudunmawa wajen inganta muhalli da matsayin kayayyakin nahiyar, don ba su damar shiga kasuwanni.

Jami'in ya ce kaddamar da tsarin ya dace da burin yankin cinikayya cikin 'yanci na Afrika, wanda ke neman kara dunkulewar nahiyar da zirga-zirgar kayayyaki da hidimomi cikin 'yanci.

Ya kara da cewa, tsarin zai kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen nahiyar da rage gwaje-gwaje da tantance kayayyaki da wasu 'yan kasuwa ke fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China