in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya bukaci a kara azamar dakile tashin hankali don cigaban Afrika
2019-03-18 11:20:33 cri
Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya bukaci kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika (AU) Moussa Faki, da a dauki kwararan matakan rigakafin tashe tashen hankula domin bunkasa cigaban nahiyar Afrika cikin sauri.

Sisi, wanda ya karbi shugabancin kungiyar ta AU a watan Fabrairu, yayi wannan tsokaci ne a lokacin ganawarsa da Faki a gefen taron dake gudana na dandalin hadin kan matasan kasashen Larabawa da na Afrika a lardin Aswan dake kasar Masar, kamar yadda kakakin ofishin shugaban kasar Masar Bassam Radi ya bayyana.

Shugaban kasar Masar ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta cigaba da yin hadin gwiwa da kuma jagorancin hukumar gudanarwar kungiyar ta AU wajen yin aikin tabbatar da hadin kan kasashen Afrika a dukkan fannoni a lokacin wa'adin jagorancinsa na kungiyar ta AU.

A lokacin ganawar, Sisi ya jaddada muhimmancin amfani da kwararan matakai da nufin cimma muhimman nasarori mafiya muhimmanci, musamman a fannin cigaban tattalin arzikin nahiyar, da samar da zaman lafiya da tsaro, da kyautata tsarin shugabancin kungiyar AU da karfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU da sauran abokan hulda na kasa da kasa.

A nasa bangaren, Faki, ya nanata muhimmancin Masar a Afrika, a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka kafa tushen kungiyar hada kan Afrika ta OAU, a matsayin kungiya ta farko data kuduri aniyar aikin cigaban nahiyar ta hanyar hadin gwiwa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China