Moussa Faki ya gabatar da shawarar ne a jiya Litinin a birnin Tripoli, fadar mulkin kasar ta Libya, yana mai cewa al'ummar kasar ne kadai za su iya yanke hukunci, game da batutuwan da suka shafi siyasar kasar. Ya kuma soki duk wani mataki na tsoma hannu wasu sassa na waje, cikin batun siyasar kasar, matakin da a cewarsa na kara dagula al'amuran kasar.
Wata sanarwa da ofishin Mr. Faki ya fitar, ta ce firaministan na Libya ya amince da wannan shawara, yana mai fatan za a gudanar da taron sulhun karkashin jagorancin MDD. (Saminu Hassan)