in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a kara jure barazanar sauyin yanayi
2019-03-04 11:25:01 cri

Tarayyar Afrika AU, ta jaddada raunin da Afrika ke da shi na fuskantar mabambantan barazanar sauyin yanayi a kan halittu da bil'adama, wadanda suke kara munana saboda abubuwa masu tsanani kamar fari da ambaliya.

Wata sanarwa da AU ta fitar a jiya, ta ce an yi hasashen cewa nahiyar Afrika ita ce ta 2 a duniya bayan yankuna masu tsananin sanyi, da za ta fuskanci tasirin sauyin yanayi.

Sanarwar ta ce yanzu haka, tasirin sauyin yanayi na tarnaki ga ci gaban tattalin arziki, ko ma a wani lokacin, ya haifar da koma baya ga ribar da aka samu cikin shekaru da dama.

Ta ce kimanin kaso 90 na annobar da ake samu a nahiyar na da alaka da yanayi, wanda kuma ke haddasa koma baya ga sakamakon tattalin arzikin kasa da kaso 10 ko 20.

A don haka AU ta ce, ci gaban nahiyar da manufofinta kan juriya da yanayi abubuwa ne ke da alaka da juna.

Ta ce shiryawa sauyin yanayi shi ne muhimmin abu ga ci gaban da nahiyar ke buri kamar su ajandar 2030 da ta 2063 da kuma muradun ci gaba masu dorewa na MDD. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China