in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci masu ruwa da tsaki a Nijeriya su ci gaba da ta zama abun misali
2019-03-02 16:00:32 cri
Shugaban hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat, ya yi maraba da yadda aka gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya cikin lumana a Nijeriya.

Cikin wata sanarwar da aka fitar jiya, Moussa Faki Mahamat, ya ce masu sa ido kan harkokin zabe na AU da na sauran kasashen waje, sun ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, bisa tsarin dokokin kasar, wanda wani muhimmin mataki ne na karfafa demokuradiyya a kasar.

Shugaban ya kuma yabawa hukumar zaben kasar wato INEC, game da yadda ta gudanar da zaben, da kuma 'yan siyasa da al'ummar kasar, bisa yadda suka fita suka kada kur'a da kuma halin dattako da suka nuna.

Moussa Faki ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a tsarin zaben Nijeriya, su tabbatar da dorewar yanayin da kasar ke ci na abun misali. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China