in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a jihar Kaduna
2019-03-14 10:31:21 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun tsaurara matakan tsaro a jihar Kaduna dake arewacin kasar dake fama da rikici, inda aka kashe mutane da dama cikin watan da ya gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojojin saman kasar, Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa, dakarunsu za su ci gaba da yin sintiri ta sama a Kaduna da kewaye.

Bugu da kari, za su hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen yin sintiri da motoci masu sulke a manyan tituna da hanyoyin jiragen kasa da sauran wuraren dake cikin jihar don tabbatar da tsaron lafiyar al'ummar jihar da ma matafiya.

Ana sa ran fadada sintirin da sojojin suke yi don wurare masu hadari a kan babbar hanyar Abuja-Kaduna wadda ta hade jihar da Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China