Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadi sakamakon ruftawar wani bene mai hawa uku na wata makarantar firamare a yankin Ita-Faji dake jahar Legas, inda ya yi sanadiyyar kashe rayuka, musamman kananan yara.
A wata sanarwa da aka fitar a Abuja, shugaba Buhari ya jajantawa iyayen yara da dangin wadanda hadarin ya rutsa da su kana ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.
Shugaban kasar ya bukaci gwamnatin jahar Legas, cibiyar kasuwancin Najeriyar, da ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kaucewa afkuwar irin hakan a nan gaba.
Wani jami'in aikin ceto a yankin ya bayyana cewa, an samu nasarar zakulo gawarwakin mutane 9 daga cikin burabuzan ginin kana akwai wasu mutanen da dama da ginin ya danne su, wanda ya hada da ginin makaranta, da shaguna da kuma wasu gidajen kwanan jama'a, wadanda ginin ya afka musu da safiyar ranar Laraba a birnin Legas.
Wani jami'i ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kimanin yara 'yan makaranta 172 ne aka yi wa rejista a makarantar, kuma kawo yanzu an ceto yara 50.
Har yanzu ba'a tantance musabbabin ruftawar ginin ba. (Ahmad)