Wata sanarwa daga hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ta ce cutar da ake samu daga ruwan sha, ya bazu ne a fadin yankunan kananan hukumomi 25 na jihar.
Hukumar ta kara da cewa, Cutar, wadda ke ja gaba wajen haifar da asarar rayuka a kasashe masu tasowa kamar Nijeriya, na kara karuwa a jihar Borno, inda yara 4,693 suka kamu kawo yanzu.
A cewar daraktan cibiyar takaita yaduwar cutuka ta jihar, Babagana Abiso, yanzu haka, ana kokarin dakile bazuwar cutar.
Kyanda cuta ce da ake samu daga hanyar kwayoyin cuta a tsakanin yara. Kuma ya kan yi tsanani har ma ya kai ga asarar rai a tsakanin yara kananan.
Jami'in ya ce, asusun kula da yara na MDD UNICEF da hukumar lafiya ta duniya WHO, za su samar da taimakon da ake bukata yayin aikin riga kafi na kwanaki 10. (Fa'iza Mustapha)