"Ba za'a taba amincewa da ci gaba da yanayin da ake ciki a halin yanzu ba wanda ya mayar da yankin kasashen Larabawa a matsayin yanki mai fuskantar tashe-tashen hankula da rikice-rikice wanda ke barzana ga tsaro, zaman lafiyar, da kuma ci gaban kasashenmu," in ji ministan harkokin wajen kasar Tunisia Khemaies Jhinaoui, yayin da yake fitar da sanarwar karshen bayan kammala taron kolin.
Game da batun kasar Syria kuwa, wanda aka yi matukar tattaunawa kansa a lokacin taron kolin, duk da cewa shugaban kasar ta Syrian bai halarci taron ba, sanarwar karshen ta tabbatar da cewa, shugabannin kasashen Larabawa za su yi amfani da matakan siyasa domin kawo karshen rikicin Syria da kuma magance matsanancin halin da al'ummar kasar ke ciki da tabbatar musu da burin da suke da shi na ci gaba da rayuwa cikin yanayin zaman lafiya da tsaro, kana da tabbatar da hadin kan kasar Syriar da ikon da kasar ke da shi na gudanar da yankunanta bisa 'yancin kai.
Sanarwar karshen ta amince da yankin nan na Golan Heights a matsayin wani bangare mallakin kasar Syria, bisa ga tsarin dokokin kasa da kasa, da yarjejeniyar kwamitin sulhun MDD. (Ahmad Fagam)