in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu ta ki amincewa da kiran da kasar Amurka ta yi na shirya taron neman gudummawar jin kai ga zirin Gaza
2018-03-12 13:26:33 cri
Manyan kungiyoyin Palesdinu ciki har da kungiyar 'yantar da Palesdinu da kungiyar Hamas da sauransu sun bayyana a ranar 11 ga wata cewa, sun ki amincewa da kiran da kasar Amurka ta yi na gudanar da taron samar da gudummawar jin kai ga zirin Gaza.

Memban kwamitin zartaswa na kungiyar 'yantar da Palesdinu Ahmed Majdalani ya bayyanawa 'yan jarida cewa, muddin ana son warware rikicin jin kai a zirin Gaza, ya kamata a fara ne da warware batun takaddamar siyasa a zirin da farko, sai kuma a tunkari batun jin kai da samar da gudummawar. Gwamnatin kasar Amurkar tana sane da dalilan da suka haifar da faruwar rikici a zirin Gaza, hakan ya faru ne a sakamakon mamayar da Isra'ila ta yi wa yankin. Mr.Majdalani ya bayyana cewa, za a iya warware rikicin jin kan idan aka soke mamayar da aka yi a zirin na Gaza. Amurka ta ba da shawarar gudanar da taron ne da nufin jawo baraka a zirin Gaza da yankin yammacin gabar kogin Jordan, da kuma nuna rashin amincewa da ra'ayin kafa kasar Palesdinu bisa shatin iyakar kasa da aka cimma a shekarar 1967.

A wannan rana kuma, kakakin kungiyar Hamas Hazem Qasem ya bayyanawa 'yan jarida cewa, kungiyar Hamas ta ki amincewa da wannan taro, kuma ba ta amince da duk sharadin da kasar Amurka ta gindaya ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China