in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Palesdinu ya jinjinawa ra'ayoyi hudu na Sin
2018-04-25 13:16:33 cri
Shugaban kasar Palesdinu Mahmoud Abbas ya jinjinawa kasar Sin, bisa gabatar da ra'ayoyi 4 da ta yi game da yadda za a warware batun kasar Palesdinu, yana mai godiya ga kasar Sin bisa goyon baya ga sha'anin Palesdinawa.

Abbas ya karbi wasika da sabon direktan sashen Sin dake kasar Palesdinu Guo Wei ya mika masa a birnin Ramalla, dake yammacin gabar kogin Jordan a wannan rana. Ya kuma jaddada cewa, al'ummar Palesdinawa na dora muhimmanci sosai ga dangantakar dake tsakaninsu da kasar Sin, yana mai fatan yin amfani da damar cika shekaru 30 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin sassan biyu, wajen fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, don daga dangantakar dake tsakanin su zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Guo Wei ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga warware batun Palesdinu a dukkan fannoni cikin adalci da mai dorewa. Ya ce, za a sa kaimi ga aiwatar da ra'ayoyi hudu da Sin ta gabatar, game da warware batun Palesdinu da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, don kokarin zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China