Abbas da firaministan kasar Iraki Adel Abdul-Mahdi sun yi shawarwari a wannan rana, bayan hakan, Abbas ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Amurka ta amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isr'ila, wannan ya shaida cewa, Amurka ba ta adalci tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
A nasa bangare, firaministan kasar Iraki Abdul-Mahdi ya bayyana cewa, kasar Iraki za ta ci gaba da tabbatar da hakkin jama'ar Palesdinu.
Bayan da Donald Trump ya zama shugaban kasar Amurka, ya yi yunkurin zartas da yarjejeniya don sa kaimi ga samun zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. A ganin Palesdinu, wannan yarjejeniya ba ta shafi batun birnin Kudus, da 'yan gudun hijirar Palesdinu, da matsugunan Yahudawa ba, don haka ba za ta amince da yarjejeniyar ba. (Zainab)