Ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shoukry, ya bayyana a gun taron manema labarun cewa, ya kamata kasa da kasa su dauki alhakin kare hakkin Palesdinawa, da sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a yankin. Ya ce, kasar Masar za ta ci gaba da yin kira da a tabbatar da hakki da moriyar Palesdinawa bisa kudurorin kasa da kasa masu nasaba da hakan.
A nasa bangaren kuwa, ministan harkokin wajen kasar Jordan Ayman Safadi ya bayyana cewa, ya kamata a warware batun Palesdinu ta hanyar siyasa, da baiwa Palesdinawa damar farfado da imanin kiyaye hakkinsu. Ya ce kasarsa ta yi Allah wadai da kasar Isra'ila, bisa illata yanayin shimfida zaman lafiya, da shirin kasashen biyu kan batun Palesdinu da Isra'ila.
Hazakalika kuma, ministocin biyu sun kalubalanci kasar Amurka, da ta dauki matakai cikin hanzari don warware batun Palesdinu da Isra'ila ta hanyar siyasa. (Zainab)