Kwamitin sulhun ya kada kuri'a game da kudurori biyu kan batun Palesdinu, wadanda kasar Kuwait da Amurka suka tsara, amma kuma ba a zartas da su ba.
Ma ya bayyana cewa, kudurin da kasar Kuwait ta gabatar, ya shaida halin da ake ciki, wanda ya taimaka wajen tabbatar da tsaron fararen hula na Palesdinu, da sassauta halin da ake ciki tsakanin Isra'ila da Palesdinu. Ya ce kasar Sin ta yabawa Kuwait bisa kokarinta na neman cimma daidaito a tsakanin bangarori daban daban, a don haka Sin ta amince da kudurin da Kuwait din ta gabatar.
Ma ya kara da cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD da kasa da kasa su dauki matakan biyan bukatun da suka dace na Palesdinu da Larabawa, da sa kaimi ga yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila cikin hanzari, da cimma burin kafa kasashen biyu don samun zaman lafiya a tsakaninsu.(Zainab)