in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta ayyana kwanaki 2 don yin makokin mutane 139 da guguwar Idai ta kashe a kasar
2019-03-22 10:17:02 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ayyana kwanaki biyu a matsayin ranakun zaman makoki a duk fadin kasar bayan da aka samu ibtila'in mahaukaciyar guguwa ta Idai wadda ta hallaka mutane 139 tare da mummunar barna a yankunan gabashi da kudancin kasar.

A jawabin da shugaban ya gabatarwa kasar a ranar Alhamis, ya bayyana ranakun 23 da 24 a matsayin ranakun makoki a duk fadin kasar.

Mahaukaciyar guguwar ta Idai, ta haifar da mummunar barna a Zimbabwe da makwabciyar ta Mozambique tsakanin ranakun Juma'a zuwa Lahadi, inda aka samu iska mai karfi da ambaliyar ruwa lamarin da ya yi sanadiyyar raba dubban mutane da gidajensu bayan da gidajen suka rushe a sakamakon ruwan sama kamar da baki kwarya.

Gwamnati ta ce, mutane sama da 150 sun bace bayan ambaliyar ruwan.

Ambaliyar ruwan ta lalata dokiyoyi masu yawa kana ta lalata kayayyaki more rayuwa kamar hanyoyin mota da gadoji, musamman a gundumar Chimanimani inda nan ne barna ta fi shafa.

A yayin da ake cigaba da aikin ceto, ana cigaba da samun gudummowa daga daidaikun mutane, kamfanoni, da gwamnatocin shiyyoyi, da hukumomin ba da agaji na kasa da kasa.

Kasashen Sin, Amurka, da tarayyar Turai, tuni suka mika tallafinsu ga al'ummonin da ibtila'in ya shafa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China