in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bada tallafin dala dubu 800 ga ayyukkan jin kai a kasar Zimbabwe
2019-03-23 15:43:12 cri

Gwamnatin kasar Sin, ta bada tallafin farin kudi dala 800,000 ga ayyukan agajin gaggawa a Zimnbabwe, domin taimakawa kasar a kokarinta na rage radadin iftila'in da ya auka mata.

Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, ya ce kasar Sin za ta bada taimakon bisa bukatun kasar da mahaukaciyar guguwar Idai ta aukawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishin jakadancin a jiya, Guo Shaochun, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta hada hannu da gwamnati da al'ummar Zimbabwe, wajen sake gina yankunan da guguwar ta lalata.

Ya kara da cewa, al'ummar Sinawa dake kasar sun ma ba a bar su a baya ba, domin sun tattara kayayyakin agaji da darajarsu ta kai dala 310,000.

Jakadan ya ce a matsayinta na 'yar uwar Zimbabwe, kasar Sin na jimami tare da al'ummar kasar, kuma har kullum kasashen biyu na tsayawa juna, sannan a shirye Sin take ta bada dukkan wani taimakon da ake bukata.

Har ila yau, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta kara bada tallafin kudi da karin rance da karfafa zuba jari a yankunan da iftila'in ya shafa, karkashin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika da kuma shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China