Guterres, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa da su da al'ummar kasar da gwamnatin kasar Zimbabwe, inji Stephane Dujarric, kakakin MDD.
Hukumar MDDr tace tana goyon bayan hukumomin kasar ta Zimbabwe kuma a shirye take tyi aiki tare dasu wajen samar da ayyukan jin kai da ake bukata wanda bala'in ya haddasa, inji sanarwar.
Mahaukaciyar guguwar ta Idai tayi sanadiyyar hallaka mutane 150 a kasashen Malawi, Mozambique da Zimbabwe, yayin da wasu daruruwan mutane suka bace.
Kakakin na mista Guterres ya gabatar da makamanciyar sanarwar ga kasashen Malawi da Mozambique a lokuta daban daban a ranakun Litinin da Juma'a.