in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bayyana cimma nasarar aikin tauraron dan Adam na Chang'e-4
2019-01-11 19:19:43 cri

Hukumar CNSA mai lura da harkokin binciken samaniya ta kasar Sin, ta tabbatar da nasarar aikin tauraron dan Adam na Chang'e-4, wadda kasar ta harba sashe mafi nisa na duniyar wata domin binciken kimiyya.

Tauraron dan Adam din ya yi aiki tare da tauraron Queqiao, da na'urar Yutu-2, inda na'urorin suka dauki junan su hotuna, wadanda aka aiko duniyar bil Adama.

Hukumar CNSA ta ce dukkanin kayayyakin binciken kimiyya da ke tare da tauraron dan Adam din suna aiki yadda ya kamata, kuma hotunan da na'urar ta dauka da sauran bayanani, na zuwa duniyar bil Adama yadda ya kamata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China