Wata sanarwa da AU ta fitar, ta ce yayin da kasashen biyu na yammacin Afrika ke daura damarar gudanar da sahihin zabe a karshen wannan makon, shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya bada umarnin tura jami'an sa ido kan harkokin zabe zuwa kasashen.
Nijeriya ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ne a gobe Asabar 23 ga wata, inda zaben Gwamnonin jihohi da na 'yan majalisun jihohi zai guda ranar 9 ga watan Maris.
Ita kuwa Senegal, za ta gudanar da zaben shugaban kasa ne a ranar Lahadi, 24 ga wata. (Fa'iza Mustapha)