Li ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar taron karawa juna sani, inda ya saurari ra'ayoyi da shawarwari da masana da masu masana'antu suka gabatar game da daftarin rahoton aikin gwamnati.
Li, kana mamban zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta hanzarta farfado da shirinta na raya kasa da zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da zurfafa samun ci gaba mai inganci.(Ibrahim)