in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya bukaci a dauki matakan daidaita ci gaba
2019-01-15 10:06:53 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su dage wajen aiwatar da matakan daidaita ci gaban tattalin arziki, bisa matsakaicin matsayi.

Li Keqiang ya yi wannan kira ne, yayin taron majalissar gudanarwar kasar na jiya Litinin, wanda aka tattauna game da rahoton yanayin ayyukan gwamnati, da ayyukan da suka jibanci raya tattalin arziki, cikin watanni uku na farkon shekarar nan ta 2019.

Mr. Li ya ce Sin na fuskantar yanayin ci gaba mai sarkakiya a bana, inda fannin neman ci gaban tattalin arzikin ta ke shan matsin lamba, wanda hakan ya sanya gwamnatin daukar matakai na wajibi, domin warware manyan kalubale.

Firaministan na Sin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki, da su kara himma wajen aiwatar da matakan daidaita yanayin ci gaba, da bunkasa kara aiwatar da sauye sauye, da gyaran fuska, da kyautata rayuwar jama'a, da kandagarkin fadawa hadurra.

Daga nan sai ya nanata kudurin gwamnatin kasar, na ci gaba da kirkirar dabaru, tare da aiwatar da manufofi mafiya dacewa, maimakon gudanar da manyan sauye sauyen tattalin arziki.

Ya ce Sin za ta wanzar da daidaiton tattalin arzikin ta bisa matsakaicin matsayi, tare da kiyaye ka'idojin da aka tsara, da kaucewa matsin lambar kasuwanni, da cin gajiya daga alfanun sauye sauye, da bude kofa ga kasashen duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China