Firaministan na Sin, wanda kuma mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya ziyarci gidajen mutane dake fama da talauci a garin Ulanqab.
Mr. Li ya bukaci sassa da batun ya shafa da su gudanar da bincike, su kuma zakulo hanyoyin bunkasa noman dankali a yankin, a wani mataki na yaki da fatara ta hanyar inganta aikin noma.
Yayin ziyararsa wata kasuwa ta manoma, Li ya ganewa idanunsa yanayin ciniki, da farashin naman shanu da na awaki. Ya ce ya zama wajibi a dauki matakan yawaita kudaden shigar al'umma, ta yadda za su samu damar kashe karin kudade. (Saminu Hassan)