Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci a kara karfafa kokarin cimma burika da kammala ayyukan da gwamnati ta shirya gamawa a bana.
Firaministan ya bayyana haka ne a jiya, yayin taron majalisar gudanawar kasar.
A cewar daftarin da aka fitar bayan taron, ya kamata sassan gwamnati su bullo da matakan cimma muhimman ayyuka nan ba da dadewa ba, ciki har da zurfafa gyare-gyare da bude kofa ga waje da kyautata ayyukan gwamnati da rage kudaden haraji.
Taron da firaministan ya jagoranta, ya jadadda aiwatar da dabarun da tsarukan aiki da aka tsara a baya, tare da fitar da wadatattun kudaden da za su taimakawa aiwatar da su.
Har ila yau, taron ya fayyace matakan rage harajin cinikayya da yanke shawarar tsawaita wasu rangwamen haraji da wa'adinsu ya kare tare da sanar da dakatar da haraji kan kamfanoni dake kashe kudi kan ayyukan rage talauci da gurbatar muhalli. (Fa'iza Mustapha)