in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun hallaka mutane 16 a Najeriya
2019-03-12 09:23:53 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga dauke da makamai, sun kai wani sabon hari a kauyen Barde na garin Maro dake yankin Kajuru a jihar Kaduna, inda suka hallaka mutane 16.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna dake yankin arewacin Najeriya Yakubu Sabo, wanda ya tabbatar da aukuwar harin na ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, 'yan bindigar sun shiga kauyen ne, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya kai ga hallaka mutanen.

Sai dai nan da nan rundunar ta tura tawagar kai dauki gami da sojoji da nufin damke bata garin tare da dawo da doka da oda a yankin.

Kakakin ya kara da cewa, jami'ansu na ci gaba da sanya ido, kuma al'amura sun daidaita. Don haka ya yi kira ga mazauna wurin da su kwantar da hankulansu. Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin na baya-bayan nan ya shafa.

Jami'in ya ce, rundunar 'yan sandan jihar ta kaddamar da bincike don gano musabbabin kai wannan harin. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China