in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uwargida Peng Liyuan ta ziyarci dakin nuna wasannin kwaikwayo na Paris
2019-03-26 14:49:34 cri

 

Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping ta ziyarci dakin nuna wasannin kwaikwayo na Paris tare da rakiyar uwargidan shugaban kasar Faransa Madam Brigitte Macron.

Madam Peng ta ziyarci dakin nuna wake-waken wasannin kwaikwayo da dakin koyon raye-raye, daga baya ta kalli shahararren wasan kwaikwayo na Die Zauberflote. Matan shugabannin kasashen biyu sun kuma zanta da 'yan wasan fasaha.

Madam Peng na fatan masu wasan fasaha na kasashen biyu za su kara cudanya da juna domin ba da babbar gudummawa ga kyautata mu'ammalar al'adun jama'arsu da ma dankon zumunci a tsakaninsu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China