in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uwar gidan shugaban Sin Peng Liyuan ta gana da Bill Gates
2018-11-06 09:19:20 cri

Uwar gidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma jakadiyar hukumar WHO kan batun rigakafi da shawo kan cututtukan tarin fuka da kanjamau madam Peng Liyuan, ta gana a jiya Litinin da shugaban hadin gwiwa na asusun Bill & Melinda Gates Foundation (BMGF) a birnin Shanghai.

A yayin ganawar, Peng Liyuan ta bayyana cewa, cikin lokaci tsawo, asusun BMGF ya zuba kudi da yawa kan ayyukan kawar da talauci da kiwon lafiya da dai sauransu, kuma yana kiyaye kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da hukumomin da batun ya shafa na kasar Sin, inda suka gudanar da hadin gwiwa a fannonin yin rigakafi da shawo kan cutar kanjamau, da ba da tallafin kiwon lafiya, da kuma inganta kwarewar jami'an lafiya na duniya. Baya ga haka, Peng Liyuan ta ce, yanzu kasar Sin na kokarin samar da kasa mai kiwon lafiyar al'umma, da kawar da talauci bisa hakikanin yanayin da ake ciki, don kaucewa haddasawa da fama da talauci sakamakon cututtuka, kana tana sa himma wajen shiga ayyukan kiwon lafiya a duniya. A cewarta, kasar Sin na goyon bayan asusun BMGF don ya ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Sin, ciki har da karfafa kwarewar ma'aikatan kiwon lafiya na Sin da na duniya baki daya.

A nasa bangaren, Bill Gates ya taya murnar nasarar bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na farko wato CIIE a takaice. Ya ce, jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a yayin bikin bude baje kolin, ya kara masa kwarin gwiwa sosai. Ya ce bisa yanayi mai sarkakiya da duniya ciki a yanzu haka, kasar Sin ta yi kokarin nuna ra'ayin bude kofa da yin hakuri da na samun moriya da nasara tare, don karfafa hadin kai da kasashe daban daban. Dan Adam na fuskantar kalubale a fannin kiwon lafiya, a cewar Gates. Ya kuma yaba sosai da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen neman ci gaba da kawar da talauci, da kuma muhimmiyar rawar da take takawa kan inganta ayyukan kiwon lafiya a duniya. Ya kuma bayyana cewa, asusun BMGF na fatan ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Sin a wadannan fannoni. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China