Peng Liyuan ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan ayyukan magancewa, da yaki da cutar AIDS, da kula da masu dauke da cutar, ta samun wasu nasarori a wannan fanni. Kana kasar Sin ta nuna yabo ga kasar Panama, bisa kokarinta a wannan fanni. Ta ce Sin ta maida hankali ga ayyukan dake shafar mata da yara, da yin kokari wajen inganta karfin bada ilmi, da tabbatar da kiwon lafiya ga mata da yara. Ta kuma yi fatan Sin da Panama za su kara samar da gudummawa wajen raya sha'anin mata da yara na kasashen biyu, har ma da na duk duniya gaba daya.
A nata bangare, Castillo ta nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin, bisa samun nasarori da ta samu wajen magancewa, da yaki da cutar AIDS, da tabbatar da hakkin mata da yara. Ta ce kasarta za ta ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin, wajen sa kaimi ga kara samun nasarori a wadannan fannoni. (Zainab)