A wannan rana da yamma, uwagida Peng Liyuan ta yi maraba da zuwan uwargida Jenni Haukio a kantin litattafai na Page One dake yankin nishadantuwa na Beijing Fang. A wannan kantin, sun saurari bayanai kan yankin Beijing Fang, da kantin litattafai na Page One, inda suka kuma gaisa da yara da iyayensu dake kantin.
Haka kuma, Peng Liyuan ta yi bayani ga uwargida Jenni Haukio kan tarihin yankin Dashilan, da kuma yadda aka kiyaye wannan yanki mai dogon tarihi.
A kantin Page One, uwargidan shugabannin kasashen biyu sun kalli nune-nunen da dalibai da malamai na jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing wato BFSU, da jami'ar kide-kide ta kasar Sin suka kawo musu.
Dalibai masu koyon harsunan Finland sun rera kasidar da uwargida Haukio ta rubuta, kuma masu wasan kayan goge na Violin da masu wasan fiyano, sun yi kida ta mai samar da kida na kasar Finland Jean Sibelius.
Kide-kide da kasidar da suka nuna wa uwargidan shugabannin biyu sun sada gadar zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu. (Maryam)