Lu Kang wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai yayin da yake mayar da martani kan zagaye na biyu na tattaunawar kasashen biyu da ya gudana a Hanoi na kasar Vietnam, ya ce yanayin da ake ciki a zirin Koriya, shi ne babban batun da ake ta magana a kansa cikin shekarun da suka gabata. Kana batun zirin na Koriya ya sake zama wani na fage na daidaita harkokin siyasa.
A don haka ya ce, kasar Sin tana fatan Koriya ta Arewa da Amurka, za su ci gaba da tattaunawa, da nunawa juna sahihanci, da mutunta juna da martaba 'yancin juna da hada kai wajen kawar da makaman nukiliya da bullo da matakan tabbatar da zaman lafiya a zirin na Koriya. (Ibrahim Yaya)