in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da mahaukaciyar guguwar Idai ta kashe a Mozambique ya karu zuwa 446
2019-03-25 08:57:47 cri
A ranar Lahadi hukumomi a kasar Mozambik sun sanar cewa yawan mutanen da mahaukaciyar guguwar nan ta Idai ta hallaka a kasar sun karu zuwa 446 wadanda aka samu a shiyyar tsakiyar kasar.

A ranar Asabar adadin mutanen da suka mutu 417 ne, amma ya zuwa ranar Lahadi adadin ya karu zuwa 446, in ji ministan filaye, muhalli da raya karkara na kasar Celso Correia, ya bayyanawa 'yan jaridu game da aikin hukumar bada agajin gaggawa ta kasar a yankin Beira, dake gabar tekun lardin Sofala, inda bala'in ya fi shafa.

Correia ya ce, abu ne mawuyaci a iya tantance adadin mutanen da suka hallaka a yankunan dake can gefe guda.

Adadin mutanen da ibtila'in ya shafa ya karu zuwa 531,466, in ji ministan, ya jaddada cewa, yawancin mutanen sun rasa gidajensu kuma har yanzu wadansu mutanen suna gararamba a yankuna bayan sun rasa matsugunansu.

"Babban abin da za'a fi mayar da hankali a cikin 'yan makonnin nan shi ne yadda za'a dakile barkewar cutuka kamar cutar kwalara, maleriya da sauran cutuka," in ji shi.

Ya ce tuni gwamnati ta tanadi cibiyoyin takaita barkewar cutukan a sassan kasar, in ji Correia. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China