Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun ya bayyana a yayin mika kayayyakin da ya gudana ranar Laraba da safe cewa, za a aika kayayyakin zuwa yankunan da bala'in ya fi tsanani dake lardin Manicaland.
Shi ma ofishin jakadancin Amurka ya sanar a jiya Talata cewa, zai raba dala 100,000 ta hukumar raya kasashe na Amurka. Yayin da kungiyar tarayyar Turai a nata bangaren ta sanar a jiya cewa, ta baiwa Mozambique taimakon gaggawa na Euro miliyan 2, sai Euro miliyan 1 ga kasar Malawi yayin da Zimbabwe kuma ta samu Euro miliyan 0.5.
A nata bangaren kasar Tanzaniya, ta aike da maganguna a ranar Talata, yayin da wasu karin magungunan daga hadaddiyar daular Larabawa za su iso kasar a yau Laraba.
Wasu daga cikin kasashen Afirka da suka yi alkawarin taimakawa, sun hada da Afirka ta kudu, Namibia da Angola. (Ibrahim Yaya)