in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mozambique ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku sakamakon mahaukaciyar guguwar Idai
2019-03-20 20:58:49 cri
Gwamnatin Mozambique ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar daga yau Laraba, don karrama wadada suka mutu sanadiyar mahaukaciyar guguwar nan mai tafe da ruwan sama ta Idai, wadda ta afkawa gabar tsakiyar kasar ta kuma haddasa ambaliya tun a ranar Alhamis din da ta gabata.

Shugaban kasar Filipe Nyusi, shi ne ya sanar da ayyana zaman makokin, bayan ganawa da majalisar ministocin kasar ranar Talata da dare a Beira, babban birnin lardin Sofala, wurin da guguwar ta fi yin barna. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China