in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahaukaciyar guguwar 'Idai' da ta yi sanadin rayuka akalla 437 a yankin kudanci Afrika
2019-03-22 10:42:52 cri

Adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Idai a yankin kudancin Afrika, ya karu zuwa akalla 437, inda jami'ai ke tsammanin sake karuwar adadin.

Gemme Connel, shugabar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD a yankunan kudanci da gabashin Afrika ce ta tabbatar da karuwar adadin.

Yayin da take ganawa da manema labarai ta wayar tarho jiya, a birnin Maputo na kasar Mozambique, Jami'ar ta ce sama da mutane 195 ne suka mutu a kasashe makwabta, da suka hada da 56 a Malawi da 139 a Zimbabwe, kamar yadda rahotanni daga gwamnatocin kasashen suka bayyana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China