in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutane da suka rasu sakamakon guguwa da ambaliyar ruwa a Zimbabwe ya kai 70
2019-03-19 10:15:14 cri

Ana ci gaba da kirga asarar rayuka da ta dukiyoyi da aka yi, sakamakon mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa ta "Idai" da ta aukawa yankunan kudu maso gabashin kasar Zimbabwe, inda kawo yanzu adadin wadanda wannan ibtila'i ya hallaka ya kai mutane 70, baya ga wasu daruruwan mutanen da suka bace.

Adadin wadanda suka rasu a yankunan lardin Manicaland sun kai mutane 65, yayin da a lardin Masvingo aka samu asarar rayuka hudu, da kuma mutum guda a lardin Mashonaland ta gabas.

Da yake karin haske game da lamarin, ministan kananan hukumomi, da ayyukan al'umma, da tsarin samar da gidaje na kasar July Moyo, ya ce mutane 65 da suka rasu a yankin Manicaland, sun rasa rayukan su ne sakamakon nutsewa a ruwa, ko raunuka da suka samu sakamakon ambaliyar ruwa.

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa, wanda ya fara wata ziyarar aiki a hadaddiyar daular Larabawa a ranar Juma'a, ya katse ziyarar ta sa, ya kuma koma gida a ranar Litinin, biyowa bayan aukuwar wannan ibtila'i.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China