in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun MNJTF sun kashe mayakan Boko Haram 50
2019-03-11 09:47:07 cri
Rundunar hadakar kasashen Najeriya, da Chadi da Kamaru da Nijar(MNJTF) da ke yakar mayakan Boko Haram, ta sanar a jiya Lahadi cewa, mayakanta sun yi nasarar kashe mayakan kungiyar 50, biyo bayan wani samame da suka kaddamar

Mai magana da yawun rundunar hadakar Timothy Antigha, shi ne ya sanar da hakan, Ya ce, dakarun rundunar da suka hada da sojojin sama da na kasa, sun kashe mayakan na Boko Haram ne, a samamen da suka kaddamar tun a ranar Jumma'a a yankin Tafkin Chadi.

Antigha ya shaidawa manema labarai a Abuja,babban binrin Najeriya cewa,rundunar za ta kara fadada hare-haren da take kaddamarwa ta hanyar kai samame, da yakin sunkuru da kai hari a lokacin sintiri domin kakkabe mayakan daga wuraren da suka rage a hannunsu a yankin tafkin Chadi.

A watan Disamban da ya gabata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tawarorinsa dake yankin tafkin Chadi suka, sake jaddada kudurinsu na kawo karshen ayyukan mayakan Boko Haram, inda suka kaddamar da "fadan a yi ta kare"

MDD ta bayyana cewa,kungiyar Boko Haram dai ta haifar da barazanar tsaro da harkokin jin kai da ma kalubalen shugabanci a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China