in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya jaddada imaninsa ga bunkasar tattalin arzikin kasar
2019-03-15 19:35:13 cri

A yau Jumma'a ne aka rufe taron shekara shekara, na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, inda aka zartas da rahoton aiki na gwamnatin kasar, da ma dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, wadda ke da niyyar kara bude kofa ga waje. Ban da wannan kuma, za a tsara jerin manufofi ba da dadewa ba, domin tinkarar tabarbarewar tattalin arzikin kasar Sin, da ma sa kaimi ga bude kofa ga waje, da yin kwaskwarima a gida. A yayin taron manema labarai da aka gudanar bayan taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, komai abun da zai faru, kasar Sin za ta dauki matakai bisa halin da take ciki yanzu, da ma hangen nesa, domin tabbatar da bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata.

Yayin da yake amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labaru na Reuters, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasarsa za ta dukufa wajen inganta kasuwa, da kara karfin yin kirkire-kirkiren kasuwa, matakin da zai tabbatar da gudanar da tattalin arziki yadda ya kamata, da kara samun ci gaba mai inganci. A cewarsa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya.

Ya kuma kara da cewa, alal hakika, kasar Sin na fuskantar sabuwar matsala sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin duniya, amma yanzu matsalar tattalin arzikin duniya ma tana kara raguwa. A cikin 'yan watannin da suka gabata, wasu manyan hukumomin duniya masu fada-a-ji, suna rage hasashensu kan kasuwar tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ma ta rage hasashenta a wannan fannin, ta kuma yi amfani da matakan daidaita tattalin arzikinta bisa matsayin da ya dace, wannan ba kawai ya hada da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta a bara ba, har ma ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta gudanar da harkokinta bisa matakan da ba su dace ba. Hakan na nuna cewa, kasar Sin ta nuna wata alama mai kyau ga kasuwar duniya.

"Yin gyare-gyare" ya zama jimla da firaminista Li ya sha ambato a yayin taron manema labaran. Ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da yin gyare-gyare ga kasuwa, domin a gudanar da harkokin kasuwanci bisa doka yadda ya kamata. Game da tambayar da wakilin kamfanin dillancin labarai na Bloomberg na Amurka ya yi masa, Li ya ce, gwamnatin kasar Sin ba ta taba sawa, kuma ba za ta sa kamfanoni su yi leken asiri a wasu kasashe ba. Ya ce irin wannan danyen aiki ya saba dokokin kasar Sin, kuma wannan ba halayyar kasar Sin ba ce.

Yayin da yake jaddada muhimmancin manufar gyare-gyare ga bunkasar kasar Sin, Li ya kuma nuna cewa, kasarsa za ta kaddamar da sabbin sassan da baki ba za su zuba jari a cikin su ba, da ci gaba da karfafa kiyaye 'yancin mallakar fasaha, da kuma ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare kamar yadda aka yi a da. Firaministan ya ce, kasar Sin na bin wani tsari kan jarin waje, wato masu zuba jari na kasashen ketare za su samu dama iri daya da takwarorinsu na kasar Sin, a yayin da suke neman zuba jari a kasuwar kasar. Baya ga haka, ban da sassan da baki 'yan kasuwa da a baya ba za su iya zuba jari ba, baki 'yan kasuwa za su samu matsayin daya da takwarorinsu na kasar Sin wajen zuba jari a kasar. A bana kuma za a kaddamar da sabbin sassan da baki ba za su zuba jari ba. Baya ga haka, kasar za ta gyara dokar 'yancin mallakar fasaha, za kuma ta kafa tsarin yanke hukunci kan wadanda suka karya dokar 'yancin mallakar fasaha.

Firaministan ya kuma nuna cewa, an zartas da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a taron shekara shekara na majalisar na bana, kuma gwamnatin kasar za ta kaddamar da jerin dokoki, da takardu bisa wannan doka, don kiyaye iko da moriyar baki 'yan kasuwa.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, rigingimun cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya jawo hankalin mutane sosai. Game da batun, Firaminista Li, ya ce yana fatan za a samu kyawawan sakamako, game da tattaunawar da ake tsakanin Sin da Amurka, kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya. Fatan kasar Sin shi ne, samun sakamakon da za su amfani kasashen biyu. Yana mai cewa, ya yi amannar shi ne abun da daukacin duniya ke fatan gani. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China