in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban tattalin arzikin Sin zai samar da damammaki ga sauran kasashen duniya
2019-03-15 19:03:56 cri

A yau Jumma'a 15 ga watan Maris ne aka rufe taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing. Duk da cewa wasu manyan hukumomin kasa da kasa sun rage hasashen da suka yi kan karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar da ake ciki, amma an lura cewa, wakilan da suka halarci taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da mambobin da suka halarci taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, suna cike imani kan karuwar tattalin arzikin kasar ta Sin, haka kuma sun gabatar da shawarwarinsu game da yadda za a cimma wannan buri, na samun karuwar tattalin arziki a kasar.

Yayin da firayin ministan kasar Sin Li Keqiang yake ganawa da menama labarai yau, ya sake jaddada cewa, ko shakka babu tattalin arzikin kasar Sin zai karu sannu a hankali, kuma za a samun karuwar tattalin arziki mai inganci kamar yadda ake fata, dalilin da sa haka shi ne, domin sabon karfin da aka samu ta hanyar yin kirkire-kirkire zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, hakan ba ma kawai zai kara kyautata rayuwar al'ummomin kasar ba ne, har ma zai samar da damammaki ga sauran kasashen duniya baki daya.

Yayin zaman taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na bana, an fitar da wasu labarai masu faranta rai, a bangaren amfanawa rayuwar jama'ar kasar da kuma kamfanonin kasar, wadannan za su kara kyautata muhallin kasuwancin kasar yadda ya kamata. Misali an zartas da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, a yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar da aka kira yau, dokar da za ta samar da tabbaci ga hakkin halal na baki 'yan kasuwa yayin da suke zuba jari a kasar Sin, tare kuma da samar da muhallin kasuwanci mai inganci da zai biya bukatun 'yan kasuwan kasa da kasa, kana za a kara rage haraji, da kuma kudin inshorar da za a biya.

An yi hasashen cewa, bayan da aka fara daukan sabbin matakan, adadin haraji, da kudin inshorar da kamfanoni, ko al'ummomin kasar za su biya zai ragu da kudin Sin RMB biliyan 2000 a cikin shekara daya. A bayyane take wadannan albishiri, za su kara cika kuzarin babbar kasuwar kasar Sin.

Jaridar The Wall Street ta Amurka ta buga wani bayani, inda aka bayyana cewa, tun farkon wannan shekara da muke ciki, darajar hada-hadar kudin kasar Sin da ake ciniki a cibiyar Shanghai ta karu da kaso 18 bisa dari, adadin da ya kai matsayin koli, tun bayan shekarar 2000. Asusun ba da lamunin kasa da kasa wato IMF, shi ma ya yaba da matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka, yana ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya dace da yanayin da kasar ke ciki, kuma shi ma zai sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasar mai inganci.

Hakika sabon karfin da aka samu, ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin tattalin arzikin kasar. A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka fitar yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar, an bayyana cewa, sabon karfin da ake amfani da shi ta hanyar yin kirkire-kirkire, ya kawo manyan sauye-sauye ga salon rayuwar al'ummomin kasar, haka kuma ya ingiza ci gaban kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.

An lura cewa, ci gaban intanet, da tattalin azikin zamani zai kawo babban sauyi ga kasuwar sayayya ta kasar Sin, shi ma zai kawo kuzari ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Bisa hasashen da rukunin tattara bayanan kasa da kasa wato IDG na Amurka ya yi, an ce, ya zuwa shekarar 2021, adadin karuwar tattalin arzikin da za a samu ta hanyar fasahohin zamani zai kai dalar Amurka biliyan 45000, adadin da zai kai kaso 50 bisa dari, daga cikin daukacin adadin karuwar tattalin arzikin duniya. A kasar Sin kuwa, adadin zai kai dalar Amurka 8500. A bayyane take cewa, kasar Sin za ta taka babbar rawa a bangaren.

Yayin taron ganawa da manema labaran da aka kira yau, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, wasu kasashe sun ga yiwuwar ci gaban sana'ar kere-kere, da sauran sabbin sana'o'in kasar Sin, zai haddasa gogayyar dake tsakanin kasa da kasa, amma wasu manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda ke da hangen nesa sun lura cewa, tabbas ne ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, zai kawo wa kasashen duniya sabbin damammaki, yayin da suke kokarin raya tattalin arzikinsu, shi ya sa ko shakka babu, za su yi amfani da wadannan damammaki ba tare da bata lokaci ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China