190313-daftarin-dokar-zuba-jari-ta-baki-yan-kasuwa-zai-samar-da-tabbaci-ga-manufar-bude-kofa-ta-sin.m4a
|
A halin yanzu wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin suna tantance daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a yayin zaman taro na biyu na majalisar karo na 13 a nan birnin Beijing, sa'an nan kuma za su jefa kuri'a kan sa. Daftarin yana da muhimmanci matuka a bangaren zuba jari na baki 'yan kasuwa, a don haka wakilai mahalarta taron suna ganin cewa, daftarin zai samar da tabbaci ga manufar kara bude kofa ga kasashen waje da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa a sabon zamanin da ake ciki yanzu.
A cikin daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwan da aka gabatarwa taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da aka saba yi, an bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kyautata manufar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a nan kasar Sin, domin samar da tabbaci gare su yayin da suke yin goyayya tsakaninsu da 'yan kasuwa na kasar Sin. Kana za ta kara karfafa aikin samar da hidima a bangaren zuba jari gare su, tare kuma da kara karfafa aikin kiyaye ikon mallakar fasahar kamfanonin da baki 'yan kasuwa suka kafa a kasar. A takaice dai ana iya cewa, za a aiwatar da manufar zuba jari ta baki 'yan kasuwa wajen ba su iznin shiga kasuwar kasar Sin, ban da bangarorin da aka hana yin amfani da jarin da 'yan kasuwar kasashen waje suka zuba.
Yayin da wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin suke duba daftarin, suna ganin cewa, idan aka kwatanta wannan daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da sauran dokoki guda uku da ake amfani da su a nan kasar Sin, wato dokar gudanar da harkokin kamfanonin da aka kafa cikin hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen ketare wajen zuba jari, da dokar gudanar da harkokin kamfanonin jarin waje, da kuma dokar gudanar da harkokin kamfanonin da kasar Sin da kasashen ketare suke tafiyar da harkokinsu cikin hadin gwiwa.
An lura cewa, daftarin ya fi mai da hankali kan manufar kara bude kofa ga kasashen waje, da kuma sa kaimi kan baki 'yan kasuwa domin su kara zuba jari a kasar Sin, kana daftarin shi ma ya ba da muhimmanci kan cudanyar halayyar musamman ta kasar Sin da ka'idojin kasa da kasa.
Wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma shugaban kungiyar sana'o'in intanet ta yankin musamman na Hong Kong Hong Weimin na ganin cewa, a cikin daftarin, an yi tanadin cewa, za a gudanar da harkokin kamfanonin jarin kasar Sin da na jarin waje bisa manufa iri guda daya, tanadin zai nuna ka'idar adalci ga 'yan kasuwa baki daya, haka kuma zai samar da muhallin karko mai adalci gare su, yana mai cewa, "Ina ganin cewa, daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa zai biya bukatun sabon zamanin da muke ciki yanzu, muna fatan kasashen duniya za su lura cewa, ana aiwatar da manufar adalci ta kasuwanci a kasar Sin, saboda daftarin zai kiyaye ikon baki 'yan kasuwa yadda ya kamata."
Alkaluman da aka samar sun nuna cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, wato tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, gaba daya adadin jarin da baki 'yan kasuwa suka zubawa kasar ya kai sama da dalar Amurka biliyan dubu biyu da dari daya, a bayyane take cewa kasar Sin ta kasance kasa mai tasowa, wadda ta fi jawo hankalin masu zuba jari a fadin duniya a cikin 'yan shekarun da suka wuce, musamman ma a shekarar 2018. Adadin jarin wajen da kasar Sin ta yi amfani da shi ya karu bisa kaso 3 bisa dari, duk da cewa adadin zuba jari kai tsaye dake tsakanin kasa da kasa a bara ya ragu bisa kaso 19 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017, wato adadin jarin waje da aka zuba jari a kasar Sin a bara ya kai dalar Amurka biliyan 138, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi.
Mambar zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma mambar kwamitin tsarin dokokin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zheng Shuna tana ganin cewa, kara yin amfani da jarin waje zai taimaka wajen kara bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da gina sabon tsarin tattalin arziki ba tare da rufa rufa ba, saboda idan ana son cimma wannan buri, dole ne a samar da tabbacin doka, tana mai cewa, "A gani na, daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da ake tantancewa yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin yana da babbar ma'ana, saboda lamarin ya nuna cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana tsara doka bisa doka da demokuradiya ta hanyar da ta dace."
A cikin wadannan shekaru 40, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri, nan gaba kuma zai ci gaba da samun bunkasuwa mai inganci, don haka ya zama wajibi a kara bude kofa ga kasashen waje.
A shekarar 2018 da ta gabata, yankunan dake tsakiya da kuma yammancin kasar Sin sun samu ci gaba a bayyane a fannin yin amfani da jarin waje, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma mataimakin shugaban kungiyar masana'antu da kasuwanci ta lardin Sichuan, kana shugaban rukunin Haite Li Biao yana ganin cewa, daftarin zai kawo karin damammaki ga yankunan dake tsakiya da yammacin kasar, ya ce, "Al'ummu a yankunan dake yammacin kasar Sin sun fi yawa, yankunan su ma suna da arzikin albarkatun halittu. Idan gwamnatin kasar Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje kamar yadda take yi yanzu, ko shakka babu za a samar mana karin damammaki."
Bisa shirin da aka tsara, za a jefa kuri'a kan daftarin a gobe ranar 15 ga watan Maris.(Jamila)