190314-Jamian-kasar-Sin-da-dama-sun-bayyana-matakan-da-za-a-dauka-domin-kara-bude-kofar-kasar-ga-ketare-luba.m4a
|
A yayin tarukan shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar (CPPCC) da ake gudanar da su a kwanakin nan, jami'an kasar Sin da dama sun bayyana matakan da za a dauka ta fannoni daban daban domin kara bude kofar kasar tare kuma da inganta hadin gwiwa da kasashen ketare.
A yayin tarukan shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar (CPPCC) na bana, yadda za a habaka bude kofar kasar ta Sin tare da daukar karin matakai na hadin gwiwa da kasa da kasa ya kasance batun da ke jawo hankalin mahalarta taron. A yayin taron majalisar wakilan jama'ar kasar da ke gudana, an duba daftarin dokar zuba jari na baki 'yan kasuwa. Mr.Liu Junchen, mataimakin shugaban kwamitin kula da dokoki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar ya ce, yadda aka nazarci daftarin dokar zuba jari na baki 'yan kasuwa a yayin taron bayan shekaru 40 da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, ya shaida niyyar kasar Sin ta inganta gyare-gyare da bude kofa. Ya ce, "Bisa ga tsarin kasa da kasa, a kan ba baki 'yan kasuwa dama daidai da takwarorinsu na gida bayan da aka amince da shigarsu cikin kasa, amma bisa ga daftarin dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, za a ba su kulawa daidai da takwarorinsu na gida ko a lokacin da suke neman iznin shiga kasa, matakin da ya kara samar da 'yanci da saukaka zuba jari."
A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta zama babban injin duniya ta fannin zuba jari ga kasashen ketare. Sai dai a cikin shekarun baya bayan nan, wasu kasashe sun tsaurara matakan bincike a kan jarin da baki suke zubawa a kasashensu, lamarin da ya kawo cikas ga kamfanonin kasar Sin da ke neman zuba jarin a ketare. Mr.Qian Keming, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, "Kullum muna kyamar duk wani nau'in kariyar ciniki, kuma ba ma son ganin daukar matakan bincike fiye da kima da za su kawo tsaiko ga baki 'yan kasuwa da suke zuba jarinsu yadda ya kamata. Muna kuma son yin hadin gwiwa tare da kasashen da abin ya shafa, domin samar da yanayi mai sauki kuma mai inganci ga masu zuba jari, domin bunkasa tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga juna."
Alkaluman sun nuna cewa, a shekarar 2018, kasar Sin ta biya kudin Sin Yuan biliyan 230 wajen shigo da fasahohin mallakar kasashen ketare, adadin da ya karu da kaso 20% bisa makamancin lokacin shekarar da ta gabata, a yayin da darajar fasahohinta da ta fitar ta kai kimanin yuan biliyan 37, wanda ya karu da kusan kaso 15%. Rahoton aikin gwamnati da aka gabatar ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar na wannan shekara ya nuna cewa, a bana, kasar Sin za ta habaka hadin gwiwa da kasa da kasa ta fannin kirkire-kirkire, kuma za ta inganta aikin kare 'yancin mallakar fasaha, tare da inganta tsarin hukunta masu keta 'yancin mallakar fasaha. A game da wannan, Shen Changyu, shugaban hukumar kare 'yancin mallakar fasahar ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Za mu yi kokarin hada gwiwa da kasa da kasa ta fannin kare 'yancin mallakar fasaha, don taimaka wa kamfanonin gida da na ketare wajen yin musayar fasahohi da kuma gudanar da ciniki, ta yadda za a bunkasa tattalin arziki mai salon bude wa juna kofa. Muna kuma wani kokari na kafa cibiyar da za ta rika ba da gudummawar kiyaye hakkin bil Adam a ketare, ta yadda ko a kasashen ketare ma za a iya ba da kariya ga 'yancin mallakar fasaha na kasar Sin."
Sauyin yanayi babban kalubale ne dake gaban kasashen duniya baki daya. Kasancewar ta kasa mai tasowa mafi girma, kasar Sin ta yi kokarin shiga aikin daidaita yanayin duniya. Ministan kula da muhallin kasar Sin Mr.Li Ganjie ya bayyana cewa, kasar Sin za ta nace ga manufarta ta tinkarar sauyin yanayi. Ya ce, "Muna goyon bayan ayyukan nazarin fasahohin rage fitar da hayakin Carbon Dioxide da kuma yayata su, ta yadda za a bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Muna kuma ba da shawarar yin rayuwa ta kiyaye muhalli da rage fitar da hayakin Carbon Dioxide. Za mu kuma yi kokarin ba da gudummawarmu wajen kula da yanayin duniya." (Lubabatu)