in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba da rahotannin da Xi ya gabatar yayin taruka biyu na bana
2019-03-14 19:43:32 cri

Yayin taruka biyu na bana, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya yi tattaunawa tsakaninsa da wakilan majalisar wakilan jama'ar kasar, da kuma mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar sau da dama, inda aka bayyana cewa, rahotannin da shugaba Xi ya gabatar sun cika imaninsu kan makomar kasar matuka.

A halin yanzu kasar Sin tana dukufa domin ingiza aikin kyautata muhallin halittu masu rai da marasa rai, musamman ma a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar. A don haka yayin da babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping yake halartar taron tantance rahotannin da aka gabatar, na tawagar wakilan jihar wadanda ke halartar zaman taro na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, ya yi nuni da cewa, ya kamata a kara karfafa aikin kiyaye muhallin halittu masu rai da masara rai, domin cimma burin dakile matsalar kazamtar muhalli, a cewarsa: "Bai kamata ba a dauki matakin raya tattalin arziki ba tare da kiyaye muhalli ba, duk da cewa kila a gamu da matsala. Yanzu haka kasar Sin tana kokarin raya tattalin arziki mai inganci, a maimakon raya tattalin arziki cikin sauri kawai, shi ya sa ya zama wajibi a kara mai da hankali kan aikin dakile matsalar kazantar muhalli, da kuma kyautata muhallin da ake ciki, domin cimma wannan burin, dole ne mu kara sanya kokari."

Kan batun, wakilin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Gong Mingzhu ya bayyana cewa, "A halin yanzu, akwai wahala mu gudanar da aikin kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai, a don haka dole ne mu yi iyakacin kokari a ko da yaushe. Idan mun daina yin kokari, kile ne kokarin da muke zai bi ruwa, shi ya sa babu sauran zabi a gabanmu, sai na bin shawarar da babban sakatare Xi Jinping ya gabatar, wato sanya kokari matuka a ko da yaushe, tabbas za mu dakile matsalolin da muke fuskantar, haka kuma za mu yi nasara."

Kana yaki da talauci da kuma farfado da kauyuka, su ne batutuwan da suka fi jawo hankalin babban sakatare Xi, yayin da yake halartar zaman taron tantance rahotannin da aka gabatar, na tawagar wakilan lardin Henan, na majalisar wakilan jama'ar kasar, Xi ya nuna cewa, aiki mafi muhimmanci yayin da ake aiwatar da manufar farfado da kauyukan kasar shi ne tabbatar da aikin samar da kayayyakin aikin gona, musamman ma tabbatar da aikin samar da abinci. A sa'i daya kuma, ya dace a sa kaimi kan gyaran fuska a tsarin samar da kayayyakin aikin gona a kasar, tare kuma da kara kyautata manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kauyukan fadin kasar, ta yadda za a gudanar da harkokin kauyukan kasar lami lafiya. Hakazalika, ya kamata a kara mai da hankali kan musanyar kwararru, da gonaki, da kuma jari dake tsakanin garuruwa da kauyuka.

Mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma mataimakin shugaban kwalejin koyar da ilmomin dokoki na jami'ar harkar kudi da tattalin arziki ta lardin Guangdong Lu Xiaoming yana ganin cewa, rahoton da babban sakatare Xi ya gabatar, ya nuna wa al'ummar kasar manufar farfado da kauyuka ta gwamnatin kasar Sin, yana mai cewa, "Babban sakatare Xi Jinping ya fahimci matsalolin da ake fuskanta, yayin da ake kokarin farfado da kauyuka a kasar Sin, haka kuma ya gabatar da shawarwarinsa kan yadda za a dakile matsalolin. Ana iya cewa, ya ba mu jagoranci mai muhimmanci. Tabbas babban sakatare Xi ya bayyana kusan daukacin matsalolin dake gabanmu. A don haka ina ganin cewa, rahotonsa ya cika imaninsu matuka. Mun hakkake cewa, za mu cimma burin farfado da kauyukan fadin kasarmu a kan lokaci."

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, za a kubutar da daukacin matalauta daga kangin talauci bisa ma'aunin da aka tsara yanzu nan da shekarar 2020. Kawo yanzu rabin gundumomin dake fama da talauci sama da 800 sun riga sun kubutar da kansu daga talauci, amma kamar yadda babban sakatare Xi ya nuna, yaki da talauci ba aiki ne mai sauki ba, saboda idan an kubutar da matalauta daga kangin talauci, dole a ci gaba da kyautata rayuwarsu nan take, ba tare da bata lokaci ba.

Wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Hou Huamei, ta fito ne daga birnin Handan na lardin Heibei, ta kuma ga yadda ake ci gaba da sanya kokari kan aikin samun wadata, bayan da aka kubutar da wasu gundumomi daga kangin talauci. Ta ce, "Hakika ana kubutar da masu fama da talauci daga mawuyacin hali bisa ma'auni na yanzu, sai dai hakan bai wuce kammala aikin yaki da talauci bisa mataki na farko ba kawai. Idan ba za a ci gaba da yin kokari ba, kile a sake shiga yanayi mai tsanani, saboda haka dole ne a ci gaba da yin kokari bisa bukatun babban sakatare Xi, wato a ci gaba da aiwatar da manufar yaki da talauci, a ci gaba da samar da taimako ga masu bukata, haka kuma a ci gaba da gudanar da aikin sa ido kan mahukuntan gundumomin da aka kubutar daga talauci, da haka za a iyar cimma burin yaki da talauci, da kuma samun wadata daga duk fannoni a fadin kasar ta Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China