in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kafa dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa domin bayyana aniyarta ta yin gyare-gayre a gida da bude kofa ga waje
2019-03-15 15:46:58 cri

Da safiyar yau Jumma'a ne aka rufe taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo na 13, inda aka zartas da dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, dokar da za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2020.

Wannan doka ta tanadi ba wa baki 'yan kasuwa iznin shiga kasuwannin kasar Sin, da kara zuba jari daga ketare, da kiyaye jarin ketare da aka zuba, da kula da yadda za a zuba jarin na ketare, wadda ta tabbatar da babban tsarin sabon salon zuba jarin ketare na kasar Sin, kuma ita ce babbar dokar ba da jagoranci kan zuba jari ta baki 'yan kasuwa a kasar Sin.

A bikin rufe taron, wakilan jama'a kusan dubu 3 sun amince da babbar dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa a kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, ta hanyar kafa wannan doka, kasar Sin ta bayyana aniyarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. Li Zhanshu, shugaban zaunannen kwamitin NPC ya bayyana cewa,"Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa da aka zartas yau a yayin taron, babbar doka ce da za ta kara azama kan bude kofar kasar Sin ga ketare yadda ya kamata a sabon zamani. Wajibi ne mu nazarce ta, mu kuma aiwatar da ita daga dukkan fannoni, a kokarin ganin ta taimaka ga bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar bude kofa ga ketare yadda ya kamata."

Jawo da kuma yin amfani da jarin waje cikin himma da kwazo, yana da muhimmanci sosai ga kasar Sin wajen kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma kafa tsarin tattalin arzikinta wanda zai bude kofa ga kowa. Don haka tabbas a ba da tabbaci ta fuskar doka.

A ganin wakilan jama'ar kasar, tabbas ne dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, za ta taimaka wajen kara kare hakkin 'yan kasuwa da ke zuba jari a kasar, da samar da mizanin yanayin kasuwanci na duniya, inda ake yin kasuwanci bisa doka kuma cikin sauki.

Huang Yushan, wani wakilin jama'a ne ya ce,"Da ma akwai wasu dokoki 3 da ake amfani da su, tun bayan da Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, amma yanzu kasarmu tana kara bude kofarta ga kasashen waje. Wannan dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa ta yi kyau sosai saboda ta biya bukatun kasarmu ta fannin samun ci gaba a nan gaba. 'Yan kasuwan waje za su kara samun adalci da hidimomi daga dukkan fannoni. Don haka na yarda da dokar. A ganina, wannan mataki ne da ya dace."

Liu Yuan, wani wakilin jama'a na daban ya nuna cewa,"Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa ya bayyana wa dukkan wadanda suke so su zuba jari a kasar Sin aniyar kasarmu ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje. Kasarmu tana maraba da su. Tabbas dokar za ta kara azama kan bunkasuwar kasarmu yadda ya kamata."

Tafiyar da harkoki bisa doka, shi ne mafi dacewa da harkokin kasuwanci. Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa, ta amsa bukatun baki 'yan kasuwa da kamfanonin waje da ke fatan zuba jari a kasar Sin. Za kuma a ba da tabbaci ta fuskar doka wajen zuba jari ta baki 'yan kasuwa, tare da samar da yanayin kasuwanci mai kyau a duniya. Bernard Dewit, shugaban kwamitin tattalin arziki da yin cinikayya a tsakanin kasashen Belguim da Sin ya yi bayanin cewa,"A ganina, dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa ta sake bayyana wa kasashen yammacin duniya aniyar gwamnatin kasar Sin ta bude kofarta ga ketare, kuma kasar Sin na maraba da 'yan kasuwa da su zuba jari a kasar. Kasar Sin za ta saukaka shigar da jarin waje cikin kasar da kuma zuba jari a kasar, lamarin da yake da muhimmanci sosai. Saboda da kiyaye hakkinsu baki 'yan kasuwa shi ne muhimmanci. Ina tsammanin cewa, dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa ta biya bukatunsu kwarai. "(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China