Firaministan kasar Sin ya ce za'a tabbatar da kara samun mutane sama da miliyan 11 da za su samu guraban ayyukan yi a birane da garuruwa
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Jumma'a cewa, bana a karon farko, gwamnatin kasar ta ayyana manufar kara samar da guraban ayyukan yi daya daga cikin muhimman manufofin gwamnatin kasar daga manyan fannoni, baya ga manufar tattalin arziki, da manufar kudade.
Firaminista Li ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai da dama, domin tabbatar da samar da guraban ayyukan yi ga wasu gungun mutane na musamman, da samar da goyon-baya ta fannin manufa, ga kamfanonin da suka iya daukar ma'aikata da yawa.(Murtala Zhang)