Firaministan ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labaru na Reuters, yana mai cewa, gaskiya kasar Sin na fuskantar sabuwar matsala sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin duniya, amma yanzu matsalar tattalin arzikin duniya ma tana kara raguwa. A cikin 'yan watannin da suka gabata, wasu manyan hukumomin duniya masu fada-a-ji suna rage hasashensu kan kasuwar tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ma ta rage hasashenta a wannan fannin, ta kuma yi amfani da matakan daidaita tattalin arzikinta bisa matsayin da ya dace, wannan ba kawai ya hada da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta a bara ba, har ma ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta gudanar da harkokinta bisa matakan da ba su da dace ba, hakan na nuna cewa, kasar Sin ta nuna wata alama mai kyau ga kasuwar duniya.
Baya ga haka, firaministan ya nuna cewa, duk wane sabon yanayi da za a fuskanta, kasar Sin tana da tabbacin samun ci gaban tattalin arzikinta yadda ya kamata a cikin dogon lokaci. (Bilkisu)